Shekarar 2023 Da Kalubalen Masu Zabe A Nijeriya – Muhammad Belgore

Nan da kusan ‘yan watanni ‘yan Nijeriya za su kada kuria’ ind azasu zabi sabbin shuwagabanni a fadin kasar, jawo hankalin alummar kasar ta cikin wannan Makala shi ne burina, kowa dai yasan hali da ake ciki ta kai ga kunnuwan  kurame ka iya jiwo kunjin ’yan kasar, idanuwan makafi na iya ganin irin azabar da ake yiwa talakawa gami da muguwar wahalarda suke kurba.

Babu bukatar tsawaitawa akan hakan. Ko da kuwa matsalar rashin tsaro ce, kawai nace babu bukatar a tsaya kan wannan batu ne saboda bazan iya ba, bamu dawani gda da yafi ta, bamu da wata kasa data fi ta, it ace duniyar mu, kada mutum ya iyakance kan sa ga iyakokin da mutum ya samar, wannan ne yasa aka ce babu inda zai iya maye mana gidan mu, duk da cewa akwai damar yin hijira, duk da zamu iya samawa kan mu mafaka a wani waje main isa, amma wajibi a gare mu mu samawa kasar mu mafita domin dorata akan turba mai kyau.

A tarihin siyasar Nijeriya, ban tunanin akwai wani lokaci da matasan kasar suka nuna sha’awar su na son shiga siyasar kamar yadda suka nuna yanzu, kuma wannan nada nasaba da halin kakanakayi da al’amuran gudanarwar kasar ke fuskanta. Zancen gaskiya shine kasancewar matasan nada yawa, kuma yawan zai iya sauya taswirar siyasar kasa, wannan tasa ya kamata matasan su taka rawa a kakar zabe mai zuwa ta hanyar mallakar katin zaben su wato PVC, kuma su tsame hannun su daga siyasa banga da daukar makamai, wannan it ace hanya daya tilo da za mu iya ceto kasar mu.

Wannan mataki dana ambata ba shi kadai mafita ba, haka kuma bai ta bace hanayr magance kalubalen da ake fuskanta ba, abin tambaya anan shine an ce ko wacce kuri’a guda nada karfi, waye daga cikin wadanna mutane dake jirin jadawalin takarda zabe? A gaskiya ba na jin akwai wani mai tunanin na gaskiya da zai amsa wannan tambaya dau sauri, wanda kuma zai iya hada wadannan ‘yan Takara kafada-kafada kuma sannan ya zabi guda daga ciki. Gaskiya wannan abin bakin ciki ne. amma bari muyi wata takaitacciyar jarabawa.

Sanin kowa ne akwai jam’iyyun  guda biyu dake da karfin magoya baya, da suka hadar da PDP da APC, sai kuma waddake biye musu baya ta ma’aikata wato  LP Labour party da kuma sauran jam’iyyu, yin Nazari kan manyan ‘yan siyasa da suka hadar da Atiku, Tinubu da kuma na ukun su Peter Obi, yayin da aka bar sauran da babu wanda ya damu da su.

Tambayar da nake son ko wanne mai kada kuri’a yayi itace, a cikin wadannan ‘yan Takara guda uku wanene zai iya bugin kurjin cewa zai kowa ayyukan cigaba ga Nijeriya? A cikin su wane ne zai yi zuciya da gaske don gyara dukkannin barnar da ta bayyana kan yadda Nijeriya ke shan wahala? Ban san amsar ba, kasancewa ban san amsar ba shine yasa na shiga damu, don muna cikin matsala mai tsanani.

Atiku Abubakar hamshakin dan kasuwa kuma tsohon ma’aikaci ne, ya taba zama mataimakin shugaban kasa amma abinda yafi daukar hankali matsayin sa na mutum na 2 shine yadda suka dingi samun sabani da ubangidansa. Abinda kawai ya cimma kenan matsayin sa na tsohon mataimakin shugaban kasa. Al’umma zasu cewa mataimakin shugaban kasa mutum ne kamar kowa da hau kan wata kujera ba tare da wani cikakken iko da yake da shi ba. Amma wanda bashi da wani cikakken ikon taya zai yaki ubangidansa, shugaban kasa. Abin birgewa, ya tattare tikitin jam’iyyar sa, ta hanyar sayen wakilai, ina tsammanin hakan yana Magana ne akan sa da kuma jam’iyyar sa, hakan ya bayyana abinda nake son fadi, amma ina fatan kun fahimci ainin hin wanna kokarin.

Sannan akwai Bola Ahmad Tinubu, zancen gaskiya yayin da na fahimci halin da ake ciki game da shekarun wannan Dan Takara da batun lafiyar sa, banyi tunanin wannan shine abinda ya kamata a sanya gaba wajen tattanawa ba game da chanchantar s ana zama shugaban kasa ba. Wannan marubucin bai damu ba koda akan keken marasa lafiya yake, abin tambaya a nan shi ne shin yana da gogewar da jajircewa gami da basirar ceto Nijeriya daga hali mai cike da rudani da kasar ke ciki? BAT yana da gogewa aiki tare da masu hankali da natsatstsun jagororin, akwai fa batun wadancan motocin na Bullion wadanda baza a iya bayyana a matsayin halak ba. Baza mu iya barin zancen Cin hanci da rashawa ba domin kowa yasan irin halin da ya sanya kasar nan.

BAT shine jagoran jam’iyyar dake mulkin Nijeriya tsawon shekaru 7. Bana tunanin za’a iya cire shi cikin kalubalen gazawar shugabanci da kasar ta fuskanta a tsawon wadannan shekaru 7.

Mene babban abinda ya tabuka a matsayin sa gwamnan jihar Anambra? Yace ya bar kudi a lalatitar gwamnatin jihar, wata kila ya kasa gane banbancin aikin Gwamna dana ma’aikacin banki, amma wadanda suka gaje shi sun ce maganar ba haka take ba, sun ce bai bar koda taro ba, saboda ya amince da kwangilar da har yanzu ba’a biya ba. Duk da haka mabiya a shafin sada zumunta na Twitter nata tallata wannan dan Takara da ake ganin bai cancanta ba, amma ya sami tikitin takarar shugaban kasa har na tsawon shekaru hudu. Wahala!

Amma duk haka wadannan sune zabuka da muke da su, ta yaya mutum zai yanke shawarar inda zai kafa tantinsa? Ina tunanin Al’umma sun yadda da batun cewa babu wani mala’ika da zai zo ya gyara mana. Gashi kuma kakar zabe na kara tunkarar mu. Abinda ya kamata mai kamata mai jifa kuri’a ya mayar da hankali kan sa shine, a cikin wadannan ‘yan takarar wanne ne ya cancanta fiye da sauran, wanda ya sami halayen shugaban da nijeriya ke bukata bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Shugaba mara tsaro mai kishin kasa wanda zai iya daukar dukkan matakin daya dake domin ganin Nijeriya ta koma cikin sahun kasashe masu tasowa, ban sanin ba ko wannan zai kasance Atiku ne, BAT ko kuma Perter Obi. Za’a fara yakin neman zabe gadan-gadan cikin kankanin lokaci. A karshe dai Ina fatan ko wanne dan takarar zai bayyana mana abinda zai mana ta hanyar bayanan sa.

Daga bisani mai kada kuri’a ya warware matsalolin sa ta hanyar yin hukunci gaskiya ba tare da sanya son zuciya ba, saboda bamu da wani wuri da zamu kira gida da ya wuce Nijeriya.

Za’a iya riskar *Belgore ta, [email protected]*

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 34 minutes 13 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 15 minutes 38 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com