Kotun daukaka kara a jihar kano dake Arewacin Nijeriya ta wanke wani matashi mai kimanin shekaru 22 Yahaya Sharif Aminu, wanda kotun shari’ar musulunci ta yanke masa hukuncin kisa, bisa laifin batanci ga Annabi Muhammadu (S.A.W).
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Aminu daya samu wakilcin lauyan sa, Kola Alapini a kotun daukaka karar, an yanke hukunci ne a ranar 21 ga watan janairun 2021, said ai bayan yanke masa hukuncin ne ya daukaka kara.
Tun da fari dai gwamantin jihar kano ta dage mayar da martini na tsawon watanni, bayan da aka gabatar da takaitacceen bayani ga mai kara a watan maris din shekarar da ta gabata.
An dai zargi Yahaya Sharif Aminu ne da yin kalaman cin zarafi ga Annabi ta cikin wata waka da aka yaka a kafar sadarwa ta whatsapp, laifin daya saba da shashe ba 382 (b) na kudin dokokin jihar kano na shekarar 2000.












