Sojoji Sun Ceto Basaraken Gargajiya na Plateau da Aka yi Garkuwa da shi
Wani basaraken gargajiya na kauyen Pinau da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato, Dokta Dadda’u Ahmad, wanda aka yi garkuwa da shi da sanyin safiyar Talata tare da direbansa, sojojin da ke aiki da rundunar ‘Operation Safe Haven’ a kauyen sun ceto shi.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Filato da Bauchi da wasu sassan Karina Manjo Ishaku Takwa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Read Also:
Wani mazaunin kauyen Hassan Pinau ya ce, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da basaraken gargajiya da aka ceto tare da direbansa a hanyarsu ta zuwa Wase.
Ya bayyana cewa jim kadan bayan samun labarin faruwar lamarin ga sojoji a kauyen, sai suka zage damtse tare da bin diddigin masu garkuwa da mutanen inda suka kwato bindigogi biyu, da babura uku.
Musa Hassan, wani ma’aikacin da ke kula da unguwanni a yankin, ya shaida wa jaridar The Nation cewa: “Ina tare da sojoji a lokacin aikin ceto. Sojoji da wasu ’yan unguwar ne suka dawo da basaraken gargajiyar kauyen da suka yi awon gaba da masu garkuwa da mutane zuwa daji.“Kowa yana farin ciki a ƙauyen yanzu. An yi musayar wuta tsakanin sojoji da maharan kafin a ceto wadanda abin ya shafa.
“Sojoji sun yi kokari. Muna rokon Allah Ya ba su ikon ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da suke yi.”
Source: The Nation
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 26 minutes 30 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 7 minutes 55 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com