Kungiyar CAN ta yi Allah-wadai da yunkurin kashe mai taimaka wa Gwamnan Bauchi
AREWA AGENDA – Kungiyar kiristoci ta Najeriya reshen jihar Bauchi CAN ta yi Allah wadai da yunkurin wasu ‘yan bindiga da har yanzu ba a san ko su wanene ba na yunkurin kashe babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Bauchi kan harkokin addinin Kirista Fasto Zakka Magaji.
Shugaban kungiyar CAN reshen Bauchi, Rabaran Dr Abraham Damina Dimeus ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an kungiyar a ziyarar jaje a gidan hadimin gwamnan da ke Birshi, al’ummar da ke wajen birnin Bauchi.
Ya ce harin ba abin da ya dace ba kuma abin takaici ne, yana mai cewa ya kamata mutane su sani cewa rayuwa abu ne mai tsarki kuma dole ne a kiyaye ta ko ta halin kaka.
Read Also:
Shugaban kungiyar ta CAN wanda ya yi godiya ga Allah da cewa ba a samu asarar rai ba yayin harin kamar yadda ba a yi garkuwa da kowa ba, ya jaddada bukatar karfafa tsaro a fadin kasar nan.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa musamman a jihar da ma kasar baki daya da su gaggauta daukar matakan tsaro musamman a yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.
Da yake yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamnan jihar Sen Bala Mohammed Abdulkadir bisa kokarin da take yi na kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar, ya ce za a iya kara kaimi kan lamarin.
Abraham Damina ya kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu lura da tsaro da kuma sa kai wajen bada bayanai game da miyagun qwai a cikin al’umma domin a ci gaba da samun zaman lafiya a jihar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 36 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 18 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com