Jihar Gombe ta Sanar da Bullar Cutar Kwalara, ta Kuma yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 10
AREWA AGENDA – A kalla mutane 10 ne suka mutu yayinda wasu 236 suka kamu da cutar kwalara a jihar Gombe.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Gombe, Dakta Abdulrahman Shuaibu, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, kan bullar cutar a jihar.
Ya ce a ranar 20 ga Satumba, 2022, adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 236, inda ya ce a shekarar 2021, jihar ta samu adadin mutane 2,373 a cikin bullar cutar guda uku a shekarar da ta gabata.
Read Also:
“A wannan shekarar, daga ranar 30 ga watan Yuni, 2022, mun samu bullar cutar kwalara a karamar hukumar Balanga, kuma saboda shiri da gaggawar da aka yi, an shawo kan ta sosai ba tare da wani tashin hankali ba.
“Muna ganin yadda ruwan sama ya kara kamari, wanda ya haifar da ambaliya a sassan jihar da dama kuma hakan ya haifar da bullar cutar kwalara a Unguwani takwas da ke fadin kananan hukumomin Balanga, Yamaltu-Deba, Nafada, Funakaye da Gombe.
“Ma’aikatar Lafiya ta Jiha ta fara aiwatar da ayyukan kiwon lafiyar jama’a cikin gaggawa don rigakafi da shawo kan cutar kwalara. Ya zuwa jiya, 20 ga Satumba, 2022, an samu karuwar masu dauke da cutar a jihar Gombe, ya zuwa yanzu an jera masu kararraki 236.” Inji shi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 40 minutes 1 second,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 21 minutes 26 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com