Matashi ya Kashe Abokinsa da Wuka Akan Abinci a Legas

Matashi ya Kashe Abokinsa da Wuka Akan Abinci a Legas

 

Wani matashi mai suna Daniel Akindele ya daba wa abokinsa Ayo Bameke wuka har lahira a lokacin da suke fafata rikici kan abinci a Abattoir Complex da ke unguwar Agege a jihar Legas.

An tattaro cewa, Akindele da Bameke, tare da wasu abokai, sukan ziyarci rukunin domin buga kwallon kafa.

A ranar da lamarin ya faru, wakilinmu ya samu labarin cewa ‘yan biyun da abokansu sun ziyarci rukunin gidajen kamar yadda suka saba.

An ce Bameke ya bar abokansa ne don sayan abinci.

Daga baya ya dawo ya gana da abokansa a harabar gidan, aka ce yana cin abinci, sai Akindele, wanda shi ma yana jin yunwa, ya bukaci a raba abincin.

An ba da rahoton cewa bukatar ta haifar da cece-kuce da ta rikide zuwa kaka-nika-yi tsakanin abokanan biyu.

A yayin rikicin da ya barke a gaban Harmony Abattoir Management Services Limited, Bameke ya yi amfani da almakashi wajen raunata Akindele.

Wani jami’in tsaro na kamfanin, Segun Ijaola, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ziyarar da ya kai wurin, ya ce Akindele ya yi galaba a kan Bameke, inda ya tattara almakashi, sannan ya daba masa wuka a kirji.

Ya ce, “matasan adadinsu hudu ne kuma tsakanin shekaru 14 zuwa 15. Kullum suna tare. Da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar, sun kasance a gaban Harmony Abattoir Management Services Limited. Wata ma’aikaciyar mu tana kan hanyarta ta fito ta dauko wani abu a falon sai ta ga daya daga cikin yaran (Bameke) kwance a kasa.

“A yayin da take kokarin sanin abin da ke damun yaron, sai ta kira abokanan ukun su tambayi abin da ya faru. Ana cikin haka ne ta gano cewa an caka ma Bameke almakashi na haihuwa a gefen hagu na kirjinsa. Bayan da Akindele ya fahimci cewa Bameke na kwance babu motsi a kasa, sai ya yi kokarin tserewa amma matar ta kama shi.

“Yayin da yake yi masa tambayoyi, Akindele ya fara ikirari. Ya ce Bameke shi ne ya yi amfani da almakashi ya yanke hannunsa kafin ya tattara almakashin ya caka masa gefen hagu na kirjinsa. Nan take ma’aikatan kamfaninmu suka garzaya da Bameke asibitin Merit da ke Agege, amma likitan ne ya tabbatar da mutuwarsa. An kai gawar zuwa dakin ajiyar gawa.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Hundeyin ya ce, “An gurfanar da Akindele a gaban Kotun Majistare ta Yaba, Legas, a ranar 13 ga Satumba, 2022, kan zargin kisan kai. Alkalin kotun ya ba da umarnin a tsare matashin daga baya.”

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 16 hours 52 minutes 44 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 34 minutes 9 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com