Home Labarai Sojoji sun Dakile Harin Gamboru Ngala, sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 19

Sojoji sun Dakile Harin Gamboru Ngala, sun Kashe ‘Yan Ta’addar ISWAP 19

A kalla mayakan kungiyar tada kayar baya ta boko haram tsagin ISWAP 19 ne suka halaka sakamakon wani barin wuta da dakarun soji karkashin rundunar Operation HADIN KAI suka kai a garin Gamborun Ngala dake jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

An ruwaito cewa dakarun hadin gwuiw na (CJTF) ne suka kai hari a ranar 11 ga watan Oktoba, a kokarin su na dakile wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’addan suka shirya kai wa sojoji yayin da suke tsaka da sintiri wani bangare na kakkabe bata garin.

Garin Gamboru, dake iyakar Nijeriya, wanda ke da tazarar kilomita 80 daga Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.

Wata majiyar asiri ta shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin chadi cewa ‘yan ta’addan sun kawo harin ne kan Babura wasu kuma kan motoci kirar Hilux dauke da bindigu, inda suka fara kai harin kan sojojin.

Majiyar tace sojojin basu yi wata wat aba suka mayar da kora, ta hanyar dakile kokarin da ‘yan bindigar abinda ya dauki tsahon mintuna 40 ana musayar wuta.

Sai dai daga bisani dakrun sojojin sun sami galaba kan ‘yan bindiga, inda suka tilasta musu hakura da kudirin da suka dauka domin tsare.

Dakarun sojin sun sami nasarar kwace wata babbar bindiga bayan sun halaka dukkan wadanda ke dauke da ita, inda suka sami damar kwace Babura 9 da wasu tarin makamai wanda suka hada da PKT, AK-47 guda 9 dare da tarin Alburusai.

Sai dai yace babu wani rahoton mutuwa daga bangaren sojojin, amma mutum biyu sun sami raunika.

PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp