Home Labarai Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta Fatattaki ‘Yan Ta’addan tare da ceto...

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta Fatattaki ‘Yan Ta’addan tare da ceto Mutane 18 da aka yi Garkuwa da su

Rundunar ‘yan sandan jihar katsina tace ta sami nasarar fatattakar ‘yan bindiga a yayin da suka farwa kauyukan Baushe da Gatakawa dake karamar hukumar Kankara a jihar.

wannan na kushe ta cikin wata sanarwa da aka raba ga manema labarai da kakakin hukumar SP Gambo Isah ya fitar a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar.

sanarwar tace ‘yan ta’addan masu tarin yawa bisa babura dauke da bindigu kirar AK 47, sun tasamma kauyukan inda suke harbi kan mai uwa da wabi, nan jami’an ‘yan sanda suka kai dauki bayan samun rahotanni bisa jagograncin baturen ‘yan sanda na kankara.

rundunar ta yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan daga kokaringudanar da mummunan harin da suka yi niya tare da kubutar da dukkannin wadanda aka yi garkuwa da su. inda  suka sami nasarar kwato babura biyar da shanu biyu.

sai dai sanarwa ta bayyana ewa ‘yan bindigar sun halaka mutum biyu mazauna kauyen baya ga raunata mutum guda. ko da yake ana kallon an hallaka ‘yan bindigar da dama kko kuma sun tsere da raunikan harbi a jikkunansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp