Wani sabon rikicin kabilanci yayi sanadiyyar mutuwar mutane 4 a sudan ta kudu kamar yadda shuwagabannin gargajiyar yankin da likitoci suka bayyana a ranar Alhamis.
Rikin ya barke ne tsakanin kabilun hausawa da abokan rikicin su kabilar da aka fi sani da Al-Hamaj, a kauyen Wad al-Mahi dake gabashin birnin Roseires dake kudancin jihar Blue Nile.
Wata majiya daga asibitin wada al-mahi ta tabbatar da cewa mutum hudu sun mutu, inda tace gawarwakin sun iso Asibitin da raunika a jikkunan su.
Sai dai shugaban hausawan Mohamed Noureddine, ya bayyana cewa yanzu haka ina cigaba da gwabza fadan, inda aka kune gidaje masu tarin yawa.
Fada tsakanin hausawan da sauran kabilu a yankin ya barke ne tun a watan Juli, in ya haifar da asarar rayukan akalla mutane 100, tare da raunata gwammai.
Rikin daya samo asali bayan da hausawan suka bukaci a basu damar jan ragamar yankin, abinda yasa mazauna yakin ke kallon kudirin matsayin neman wurin zama ga hausawan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 15 hours 4 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 46 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com