Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina ya Fice da APC zuwa APC

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina, SSG Mustapha Inuwa, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Inuwa, wanda ya sha kaye a yunkurinsa na neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC, ya bayyana sauya shekar ta sa zuwa PDP ne a yau Lahadi a Katsina, yayin da ya ke jawabi ga magoya bayansa.

Ya bayyana cewa ya dauki matakin ne bayan tattaunawa da magoya bayansa a fadin jihar

Inuwa wanda ya yi aiki a matsayin SSG a gwamnatin Gwamna Aminu Masari daga 2015 har zuwa zaben fidda gwani na gwamna a watan Mayun 2022, ya yi ikirarin cewa an mayar da shi saniyar-ware a duk harkokin APC a jihar.

“Idan za a iya tunawa, a lokacin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC a jihar, mun san duk abin da ya faru a wancan lokacin, kuma a karshe an bayyana wanda ya yi nasara.

“Mun amince da shan kaye kuma mun yi alkawarin mara wa dan takarar jam’iyyar baya, bayan da ya ziyarce ni kuma na ba shi tabbacin goyon bayan da ya dace.

“Amma abin takaici, tun a wancan lokacin, ba a taba tuntuɓa ta da wata harka da ta shafi ci gaban jam’iyyar a jihar Katsina ba, wanda hakan ya sa a ka maishe mu saniyar-ware a jam’iyyar.

“Wannan alama ce karara cewa ba a ɗaukar mu a matsayin cikakkun ƴan APC, bar ta kai ga wasu ma na cewa za su iya cin zabe ko ba mu.

“Duba da wannan yanayi, mun gamsu cewa ba za mu iya jure zama a haka ba. Sabo da haka Ni da ɗaukacin magoya baya na mun sauya sheƙa zuwa PDP,” in ji shi.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 9 minutes 55 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 51 minutes 20 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com