Home Labarai Kotu ta Tura Masu Tiktok 2 Gidan Yari Saboda Sukar Gwamna Ganduje

Kotu ta Tura Masu Tiktok 2 Gidan Yari Saboda Sukar Gwamna Ganduje

Kotu ta Tura Masu Tiktok 2 Gidan Yari Saboda Sukar Gwamna Ganduje

 

An gurfanar da wasu masu sana’ar TikTok guda biyu Mubarak Muhammad (Uniquepikin) da Nazifi Muhammad a gidan yari bisa zargin bata sunan gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a daya daga cikin wasannin barkwanci da suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan biyun sun yi zagon kasa inda suka nuna gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin dan siyasa mai cin hanci da rashawa, wanda ya siyar da duk wani fili na jama’a a jihar.

‘Yan sanda sun gurfanar da su a gaban kotun majistare mai lamba 58, Nomansland, karkashin jagorancin Alkalin Kotun, Aminu Gabari.

Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen, TikTokers biyu sun amsa laifin da ake tuhumar su da su na hada baki da kuma bata sunan gwamnan.

Don haka alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba domin yanke hukunci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp