Za’a girke Jami’an ‘yan sanda, biyo bayan dawo da jigilar fasinjoji a jirgin kasa daga Abuja zuwa kaduna.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi, mnipr, mipra ya fitar a birnin tarayyar kasar Abuja mai dauke da kwanan watan 4 ga watan Disamba 2022 da aka akewa PRNigeria.
Sanarwar tace babban sefeton ‘Yan sanda Nijeriya Usman Alkali Baba, psc(+), NPM, NEAPS, fdc, CFR, ya bada umarnin girki Jami’an kwantar da tarzoma na Mobile Force, K-9, Force na kwarru da kuma Jami’an ‘yan sandan layin dogo domin gudanar da ayyukan tsaro kan hanyar jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ranar litinin 5 ga Disambar 2022.
Inda sanarwa ta kara da cewa Rundunar ‘yan sandan Nijeriya na cigaba da tattaunawa da hukumar dake lura da Jiragen Kasan Nijeriya da sauran Jami’an tsaro domin gudanar da aikin tsaron Al’umma yadda ya kamata.
Dakarun zasu lura da muhimman wuraren na tashar jirgin kasar da hanyar da yake bi da kuma bada shawarwari don samar da ingantacce tsaro ga fasinjoji da dukiyoyin su ta hanyar kare su ga dukkan abinda kaje kazo
Babban Sifeton ‘yan sanda ya kuma tabbarwa da Al’umma kasar musamman fasinjojin jirgin kasar cewa zasu kare su da lafiyar su da dukiyar su da zarar sun hau kan hanya domin yin balaguro, dama sauran fasinjojun dake kan jirgin kasa a dukkan fadin kasar.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 19 minutes 2 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 27 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com