Home General Dakarun Sojin Nijeriya sun Sake Hallaka ‘yan Bindiga a Jihar Kaduna

Dakarun Sojin Nijeriya sun Sake Hallaka ‘yan Bindiga a Jihar Kaduna

Dakarun sojin Nijeriya sun sake samun nasarar tarwatsa maboyar ‘yan bindiga a wani artabu da sukayi a Giwa dake jihar Kaduna.
Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mata da kanana yara bayan tarwatsa maboyar.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da Al’amurran cikin gida Samuel Aruwan ya fita.
Sanarwar tace Dakarun sojojin Nijeriya na musamman sun sake samun nasara kan ‘yan Ta’adda inda suka hallaka 9 bayan bata kashi a karamar hukumar Giwa ta Jihar.
A yayin da take bayyana rahoton tsaro Gwamnatin jihar kaduna tace dakarun su tarwatsa gungun ‘yan bindigar a maboyar su dake Rafin Sarki inda suka dakume biyar daga cikin su yayin da ragiwar suka tsere don tsira da rayukan su.
A wani bangare na gudanar da atisayen kawar da ‘yan Ta’addan dakarun na musamman sun sami nasarar tarwatsa maboyar su a Galadimawa inda dakarun suka hallaka hudu daga ciki gami da ceto mata da kananan yara da sukayi garkuwa da su.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yaba da kokarin dakarun sojin bisa namijin kokarin da sukayi na ceto wadanda akayi garkuwa dasu.
Gwamnatin jihar ta kuma bukaci Al’umma da su cigaba da tallafawa da bayanan sirri kan maboyar ‘yan Ta’addan dama masu kai musu bayanan sirri ta wadannan lambobi waya:

09034000060
08170189999

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp