Home General Dakarun sojin Saman Nijeriya sun Halaka ‘Ya Ta’adda sama da 60 a...

Dakarun sojin Saman Nijeriya sun Halaka ‘Ya Ta’adda sama da 60 a jihar Zamfara

Dakarun sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta da jirage kan sansanin ‘yan bindiga dake kauyen Mutumji a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara, abinda yayi sanadiyar kashe hallaka akalla 60 daga cikinsu.

Rahotanni sun ce daga cikin mutanen da harin ya ritsa da su harda mata da kuma yara wadanda suke yankin lokacin da harin.

Bayanai sun ce harin ya biyo bayan koken da mazauna kauyukan Malele da Ruwan Tofa da ‘yan awaki suka gabatar na cewar ‘yan bindigar sun farwa garuruwansu, abinda ya sa sojojin daukar matakin kai musu dauki ta sama.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da aukuwar lamarin, yayin da ya kuma bayyana mana cewar yayin kai daukin ta sama sojojin cikin kuskure sun hallaka wasu daga cikin abokan aikin su dake kai hari ta kasa.

Majiyar tace yayin da ake wannan, wasu yan bindigar sun yiwa tawagar sojoji kwantar bauna inda suka kaiwa motocinsu guda 3 hari a yankin.

Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar munanan hare hare daga ‘yan bindiga wadanda ke sanyawa garuruwa haraji domin hana kai musu hari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp