Dakarun rundunar sojojin Nijeriya sun kama mataimakain kwamandan mayakan kungiyar ‘yan awaren Biyafara IPOB Nwagwu Chiwendu, wanda ke hannun bisa kisan dan siyasar yankin Arewacin kasar Ahmed Gulak.
PRNigeria ta tattaro cewa Chiwendu shine mai horas da dakarun kungiyar sarrafa makamai, wanda ke matsayin na biyu cikin masu fada aji a tawagar, wanda kuma shine shugaban kungyar a jihar Imo.
Hamshakin dan Ta’addan ya bar aikin cikin rundunar soji Nijeriya, inda ya koma cikin kungiyar ta IPOB tun watan janairun 21.
“yayin aiki a cikin rundunar Operation hadin kai (OPHK) yana kuma cikin wanda suka sami horo, an kama shi jiya yayin bikin binne mahaifinsa a Mbaise. Ya kuma kai mu zuwa sansanin sun a Obowo da daddare.
“ya amsa cewa shine ya hallaka Gulak, ya kuma tabbatar da cewa sansanin ke da alhakin yin garkuwa da matafiya 2 akan hanyar Owerri zuwa Okigwe inda suka hallaka sifeton ‘yan sanda guda biyu dake musu rakiya.
haka kuma suke majiyar ta bayyanawa PRNigeria cewa, “sun eke da alhakin hallaka sojoji a wannan yanki tare ga kone motarsu kirar Hilux makon daya gabata. Haka kuma sun bada gudunmawa wajen kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta na INEC dake Owerri. Hanzu haka dai yana hannun jami’an ‘yan sanda.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 11 hours 4 minutes 24 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 12 hours 45 minutes 49 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com