Home Labarai ‘Yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron sa kai 6 a jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron sa kai 6 a jihar Kaduna

Rahotannin daga jihar Kaduna na bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron sa kai na bijilanti 6 a shingen binciken ababawan hawa na Awaro dake yammacin birnin-Gwari, a karamar hukumar birnin Gwari ta jihar Kaduna dake arewa maso yammacin Nijeria.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar laraba.
Guda cikin Jami’an bijilantin Usman Babangida, ya tabbatarwa da maneman labarai mutuwar abokan aikin nasa a ranar laraba sakamakon harin ‘yan bindiga a shingen binciken Ababan hawa da suke gudanar da ayyukan su.
Inda yace ‘yan bindigar sun fara harfi kan mai uwa da wabi bayan sun hangi jami’an na bijilanti, in da suka hallaka 6 daga cikin su, ya kuma ce wadanda aka hallaka din anyi jana’idar su kamar yadda addinin musulunci yayi tanadi.
Yace lamarin ya faru ne jim kadan bayan da ‘yan bindiag suka yi wani artabu da wasu ‘yan bindiga a wani kauye dake kusa da sum ai suna Bugai.
Ko da PRNigeria ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Kaduna Muhammad Jalige ta wayar tarho bata same shi ba.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp