Home Labarai Mutum 5 sun kone kurmus a wani hadarin mota a Badagry zuwa...

Mutum 5 sun kone kurmus a wani hadarin mota a Badagry zuwa Seme

Wani hadarin mota akan babbar hanyar badagry zuwa Seme a jihar legas yayi sanadiyar konewar mutane biyar tare da raunata da dama a ranar Alhamis.

Kwamandan hadakar jami’an hukumar kiyaye haddura ta dake badagry Mista Sulaiman Taiwo ya tabbatar da faruwar hakan ga kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN).

Inda yace hadarin yace hadarin ya auku ne a kauyen Akoro, dake daura da babbar hanyar badagry zuwa semi a jihar ta legasa dake kudu masu yammacin Nijeriya.

Hadarin ya auke ne tsakanin wata mota mai kirar Honda Pilot SUV dake da lamba LSR 772 HE da wani babur da aka kasa gane lamabr dake jikin sa.

Taiwo yace direban motar na gudun wuce sa’a ne, inda ya kasa sarrafa motar abinda ya sanya shi dukan mai babur din dake dauke da man fetur. Wannan ne ya sanya tashin wuta a yayi tawo mu gama tsakanin motar da babur din.

Mutum 3 da suka tsira da raunika a jikkunan su na karbar kulawa a babban asibitin Badagry, haka kuma gawarwakin mutum 5 kuma an kai su dakin ajiyar gawa na asibitin” a cewar sa.

Taiwo ya kara da cewa daukin gaggawa da jami’an kwastom dana kasha gobara gami da jami’an tsaro na civil defence da ‘yan sanda sukayi ya taimaka wajen dawo da wurin da lamarin ya auku yadda ya kamata.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp