Jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ayyana zaɓen da aka yi a matsayin wanda bai cika ba, kwace aka yi mata domin kuwa ta ci zaɓe.
Read Also:
A wani yanayi na hayaniya wakilan jam’iyyu da dama sun rika bayyana rashin amincewarsu da sakamakon zaɓen baki daya, bayan bayyana zaɓen karamar hukumar Fufore.
Cikin bayanin da baturen zaɓen ya yi ya ce, an soke wasu zaɓuka da aka yi a wasu kananan hukumomi masu yawa, wanda adadinsu za su iya maye tazarar da ke tsakanin ‘yan takarar APC da PDP da ke kan gaba a fafatawar.
Baturen zaɓen ya bayyana rashin cikar zaɓen lokacin da ake tsaka da hayaniya kuma ya fice daga zauren tattara bayanan.