Dan takarar gwamnan jihar Katsina na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, a zaben da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Dan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe ta bayyana.
Cikin wata hira da ya yi da BBC, Sanata Lado, ya ce, zabe ne mai cike da magudi, da aringizon kuri’u, da barazana ga masu zabe, da dai duk wani ha’incin da bai taba gani a harkar zabe ba.
Ya ce,” Ba mu gamsu da wannan sakamakon zabe ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaba bane aka bayyana.”
Dan takarar gwamna na jam’iyyar ta PDP, ya ce, yakamata a daina yin zabe kawai a rinka yin nadi, don yana ga hakan ya fi alkhairi.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1486 days 7 hours 27 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1468 days 9 hours 9 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com