Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta ce ta saka ranakun da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun gwamnoni a jihohin ƙasar da aka gudanar da zaɓen gwamna.
Read Also:
A wata sanarwar da hukumar INEC din ta fitar mai ɗauke da sa- hannun shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu kada ƙuri’a na hukumar Festu Okoye, ta ce sashe na 72 (1) na dokar zaɓen ƙasar ta 2022, ya ɗora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun ‘yan takara a cikin kwana 14 da yin zaɓen.
A kan haka ne hukumar ta ce ta saka ranar Laraba 29 ga watan Maris da kuma 31 ga watan na Maris a matsayin ranar da za ta bayar da takardar shaidar cin zaɓen ga zaɓaɓɓun gwamnoni da mataimakansu, tare kuma ‘yan majalisun dokokin jihohi.
Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaɓen ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar.
Hukumar zaɓen ta ce kwamishinonin INEC na jihohi da ma’aikatan hukumar za su sanar da zaɓaɓɓun takamammiyar ranar da za su karɓi takardun shaidar.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 50 minutes 44 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 32 minutes 9 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com