Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ƙaryata rahotonni da ke zargin dakarun sojojin ƙasar da kashe ƙananan yara a yaƙin da rundunar ke yi da mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.
Idan za’a iya tunawa a watan Disamban bara ne kamfanin dillancin labarai na Reuters a wani rahoton bincike da ya fitar ya zargi sojojin Najeriyar da gudanar da wani shiri a asirce na zubar wa da aƙalla mata 10,000 ciki.
Waɗanda suka kuɓuta daga hannun mayaƙan Boko Haram a yankin arewa maso gabshin ƙasar.
Rahoton ya ce tun a shekarar 2018, sojojin Najeriyar ke gudanar da shirin a asirce na zubar wa da matan ciki ba bisa ƙa’ida ba a yankin.
Lamarin da rahoton ya ce ya sa an zubar wa da mata akallan 10,000 ciki tsakanin manyan mata da ‘yan mata, waɗanda mayakon Boko Haram suka yi wa fyade bayan yin garkuwa da su.
Read Also:
Rahoton dai ya ja hankalin ƙasashen duniya, inda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta gudanar da gagarumin bincike tare da ɗaukar matakan da suka dace don hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
To sai babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya Laftanar Janar Faruk Yahaya ya ce sojojin Najeriya na ɗaya daga cikin rundunonin soji mafi inganci a faɗin duniya, wadanda ya ce suna gudanar da ayyukansu ta hanyar bin doka tare da kare ‘yancin ɗan adam.
Yayin da yake magana a wajen ƙaddamar kwamitin bincike na musamman kan tauye haƙƙin ɗan adam a lokacin yaƙi da ta’addanci na yankin arewa maso gabashin ƙasar da aka yi wa laƙabi da (SIIP-North East).
Janar Yahaya ya ce ”dakarun sojin ƙasar ƙwararrun dakaru ne waɗanda ke aiki bisa turbar doka, kuma ƙarƙashin zaɓaɓɓiyar gwamnatin, inda shugaban ƙasa da sauran hukumomin tsaro duka suke nan, don martaba doka, duka mun san wannan.”
Yayin da yake ƙaryata rahoton zubar wa da matan cikin, Janar Yahaya ya zargi kamfanin dillancin labaran da rashin bayyana haƙiƙanin abin da ke faruwa na mamayar da sojojin suka yi ƙungiyar a shekarun baya-bayan nan.
Ya ƙara da cewa yankunan da rahoton ya ambato cewa an aikata wannan laifi, wurare ne da ke cikin matsanancin tsaro, waɗanda ake buƙatar rakiyar soji kafin shiga cikinsu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 48 minutes 13 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 29 minutes 38 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com