Home Labarai Kotu ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin Shugaban PDP

Kotu ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin Shugaban PDP

Wata Kotu da ke zamanta a birnin Makurdi ta bai wa Dr Iyorchia Ayu umarnin daina nuna kansa a matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP a Najeriya.

Alƙali Wilfred Kpochi wanda ya bayar da umarnin, ya buƙaci Ayu ya janye daga shugabancin jam’iyyar har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da tuni aka shigar.

Tun farko, ƙarar da Injiniya Conrad Utaan ya shigar ta nemi kotu ta hana Ayu daga bayyana kansa a matsayin shugaban PDP kasancewar dakatarwar da aka yi masa.

PDP ta dakatar da Ayu NE bisa zargin sa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.

Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke ƙaramar hukumar Gboko, a jihar Benue ne suka ɗauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kaɗa ƙuri’ar rashin ƙwarin gwiwa kan ayyukansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp