Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Nijeriya ta bukaci musulmin kasar dasu fara duban watan Shawwal na shekarar 1444 (H) daga yammacin 29 ga watan ramadan wanda yayi daidai da 20 ga watan afrilun 2023 (M).
Read Also:
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke sa hannun daraktan gudanarwa na majalisar Zubairu Haruna Usman-Ugwu, wanda yace mai alfarma sarkin musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ne yayi kiran ga kwamitin duban watan na kasa wato (NMSC).
Sanarwar tace idan aka ga watan kuma aka tabbatar da sahihancin ganin sa, sarkin na musulmi ya ayyana ranar jama’a 21 ga watan afrilun 2023 matsayin 1 ga watan shawwal kuma ranar idin karamar sallah.
Haka kuma idan ba’a ga watan bay a zama ranar Asabar 22 ga watan na Afrilu matsayin ranar idan na karamar sallah.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 39 minutes 59 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 21 minutes 24 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com