Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da kama ‘yan daba da masu ƙwacen wayoyi da aka fi sani da ‘yan ‘Sara-Suka’ 98 a jihar.
Gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai ne ya buƙaci ɗaukar tsattsauran mataki kan ɓata-garin, sakamakon ƙaruwar ayyukan ‘yan daba da masu ƙwacen wayoyi a ƙwaryar birnin Kaduna.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar ya ce an gurfanar da 19 daga cikinsu a gabon kotu, yayin da ake ci gaba da bincike kan mutane 61, kafin a gurfanar da su.
Ɓata-garin kan farmaki mutane tare da ƙwace musu wayoyi da sauran kayayyaki, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka tare da jikkata mutane masu yawa.
Read Also:
Rahoton kamen wanda ‘yan sanda suka fitar, ya ce an kama ‘yan dabar a ranakun 26 da 28 ga watan Afrilu.
Rahoton ya ce 18 daga cikin ɓata-garin an kai su sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin faɗaɗa bincike, gabanin gurfanar da su a gaban kotu.
Gwamnan jihar ya umarci rundunar ‘yan sandan da su tabbatar da yin abin da ya dace domin gurfanar da su a gaban kotu, tare da faɗaɗa bincike don kamo duk masu aikata irin wannan ta’asa a faɗin jihar.
El-Rufai ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, sanadiyyar ayyukan ‘yan bindigar.
Daga ƙarshe gwamnan ya yi kira ga al’umma musamman mazauna unguwannin da ake wannan ta’asa da su kai sunayen ‘yan dabar da ke addabar yankunansu ga jami’an tsaro domin a bibiye su.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 23 minutes 47 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 3 hours 5 minutes 12 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com