Home Labarai Sudan na gab da rugujewa -MDD

Sudan na gab da rugujewa -MDD

Majalisar Dinkin Duniya tace kasar Sudan na gab da rugujewa ganin yadda ake ci gaba da samun amon wuta da karar fashe fashe a birnin Khartoum, duk da tsawaita tsagaita wutar da bangarorin dake rikicin kasar suka sanar a jiya.

Tuni wannan rikici wanda ya shiga mako na 3 ya tilastawa dubban yan kasar Sudan tserewa zuwa kasashen makota irin su Masar da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka domin samun mafaka.

Akalla mutane sama da 500 aka tabbatar da mutuwar su a wannan rikici da ya barke tun daga ranar 15 ga watan jiya, tsakanin shugaban soji Janar Abdel Fateh al-Burhan da mataimakin sa kuma shugaban jami’an tsaron kai dauki na RSF, Mohammed Hmadan Daglo.

Miliyoyin mazauna birnin Khartum sun makale a cikin gidajen su yayin da suke fama da rashin abinci da kuma ruwan sha, yayin aka katse wutar lantarki, sai kuma jiragen yakin dake ci gaba da shawagi suna kai hare hare ba tare da kaukautawa ba.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa a Khartoum yace ko ayau litinin an ga jiragen yaki na shawagi a kudancin birnin, yayin da mayakan Daglo ke kai musu hari da makaman kakkabo jirage.

Kasashen duniya kuma sun mayar da hankali ne wajen kwashe mutanen su da wannan rikici ya ritsa da su, yayin da alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna cewar ya zuwa yanzu an kwashe baki sama da 50,000.

Daliban Najeriya na cikin dubban yan kasashen waje da suke fatan ganin an mayar da su gida tun bayan barkewar rikicin, amma har ya zuwa wannan lokaci babu koda mutum guda da aka mayar gida.

Sai dai Babban sakatare a ma’aikatar jinkai ta Najeriya, Dr Nasir Sani Gwarzo yace sun sake fasalin kwashe daliban, kuma yanzu za suyi amfani da tashar Port Sudan ne.

Ya zuwa yanzu iyayen wadannan dalibai na cikin zulumi ganin yadda yakin ke ci gaba da kazancewa, yayin da kasashen duniya suka kasa shawo kan hafsoshin dake rikicin.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp