Home Labarai Sojojin Nijeriya sun sake kubutar ‘yan matan Chibok

Sojojin Nijeriya sun sake kubutar ‘yan matan Chibok

Dakarun Sojojin Nijeriya sun sami nasarar sake kubutar da karin ‘yan Matan Chibok tare da hallaka ‘yan Ta’ adda 40 – DHQ

Shalkwatar rundunar sojin Nijeriya tace dakarun hadin Guiwa na Operation HADARIN DAJI, dake aikin samar da tsaron a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, sun sami nasarar kama ‘yan Ta’adda 5 tre da kubutar da fararen hula 121 da suka hadar da yara 72 da mata 49 cikin su akwai ‘yan matan makarantar Chibok 2.

Babban hafsan sojojin kasar Laftanal Janar Lucky Irabor ne ya bayyana  hakan yayin da yake bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu kamar yadda aka saba mako mako.

Daraktar yada labaran rundunar Manjo Janar Musa Danmadani yayi jawabi dalla-dalla bisa ayyukan dakarun, inda yace dakarun sojin sama dana kasa dake cikin rundunar Operation HADARIN DAJI dake gudanar da ayyukan su a yankin Arewa maso yammacin kasar sun kama wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne masu safar kwayoyi a kauyen Wazata dake karamar hukumar birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Haka kuma a Arewa maso gabashi dakarun sun sami nasarar hallaka mayaka Boko Haram dana ISWAP 40, tare da kama 25 wanda suka hadar da masu yi musu safarar kayayyaki da baya ai a lokacin da suka shirya kai hare hare kan kauyuka da dazukan garuruwan Gwoza, Bama, Biu, Kukawa, Monguno, Marte, Damboa, Mobbar da yankunan karamar hukumar Konduga a jihar Borno State.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp