Gwamnatin Najeriya ta amince a jinginar da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da kuma Mallam Aminu Kano da ke Kano.
Gwamnati ta amince da wannan mataki ne a taron majalisar koli da aka gudanar jiya a Abuja.
Read Also:
Ministan sufirin jiragen sama a Najeriya, Hadi Sirika, ya shaidawa manema labarai cewa za a jinginar da filin jirgin Abuja na shekara 20, sannan na Kano na tsawon shekara 30.
Sirika ya ce taron nasu ya kuma amince a sauyawa ma’aikatarsu suna daga ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama zuwa ma’aikatar kula da sufirin jiragen sama da sararrin samaniya.
Ya kuma ce taron ya amince da wasu tsare-tsare da za su inganta harkokin sufirin jirage a Najeriya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 19 hours 56 minutes 12 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 21 hours 37 minutes 37 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com