Home DUNIYA Yankin Sahel na bukatar kudaden yaki da masu tsattsauran ra’ayi- MDD

Yankin Sahel na bukatar kudaden yaki da masu tsattsauran ra’ayi- MDD

Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da nahiyar Afrika Martha Pobee, ta koka da yadda yankin Sahel ke matsayin matattarar ayyukan ta’addanci sakamakon yadda ake ganin karuwar tashe-tashen hankula da ke da nasaba da masu tsattsauran ra’ayin addini bayan gazawar rundunar hadin gwiwa wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda da ya ta’azzara rashin tsaro a yankin.

Martha wadda ita ce mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da nahiyar Afrika, ta bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar tsaro, wanda ya tattauna kan yadda za a yaki kungiyoyin ta’addanci da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaida.

A shekarar 2014 ne aka samar da rundunar hadin gwiwa tsakanin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mauritania da kuma Nijar, ganin cewa a shekarar da ta gabata Mali ta fice daga cikin wannan tafiya.

Sai dai a cewar Pobee tun a watan Janairun da ya gabata, rabon da rundunar ta gudanar da wani gagarumin aiki, saboda kintsawa don tunkarar sabbin kalubalen da ke gaban ta, wanda ke da nasaba da rashin kudaden tafiyar da harkokinta kama daga yaki da ‘yan ta’addan kai tsaye da kuma rage tsaurin akida tsakanin jama’ar yankin.

A baya-bayan nan ne Burkina Faso da kuma jamhuriyar Nijar, suka sake inganta alakar su da Mali, don tunkarar kalubalen tsaro a iyakokin kasashen su.

Jami’ar ta yi gargadin cewar rashin cimma wata jituwa tsakanin kasashen waje abokan huldar su ne ya sanya rundunar ta gaza samun gudunmuwar kudi don gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata.

Toh sai dai shugaban kungiyar kasashen G5 Sahel Eric Tiare, ya ce an kammala tsara sabbin shirye-shiryen yadda rundunar za ta rinka gudanar da aikin ta, wanda za a mikawa majalisar tsaro da kuma kungiyar tarayyar Afrika don amincewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp