Home Labarai An fara cinkoson sayen fetur a Nijeriya sakamakon kalaman Tinubu

An fara cinkoson sayen fetur a Nijeriya sakamakon kalaman Tinubu

An fara dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur da ke birnin Lagos na Najeriya jim kadan da sanarwar da shugaban kasar, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta janye kudin tallafin man fetur.

Manema labarai sun rawaito cewa, direbobin motoci sun yi cincirindo a gidajen mai na NNPC da ke Ikeja, inda suke rige-rigen sayen man.

da dama daga cikin gidajen man fetur masu zaman kansu ba sa sayar da man ya zuwa lokacin da fitar da rahoton.

A yayin gabatar da jawabinsa na shan rantsuwar kama aiki a yau Litinin, shugaba Tinubu ya bayyana cewa, mawadata ne kadai ke amfana da kudin tallafin man fetur din a maimakon talakawa.

Tinubu ya ce, gwamnatinsa za ta karkatar da kudin tallafin zuwa ga bangarorin ilimi da lafiya da samar da ayyuka da gina kayayyakin more rayuwa da za su amfani miliyoyin al’umma.

Kazalika shugaban ya ce, zai nazarci korafe-korafe game da dimbin kudaden haraji don ganin an habbaka tattalin arzikin kasar tare da janyo masu zuba jari.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp