Gwamnan jihar kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin gyarawa da inganta cibiyar gyaran hali da tarbiyya deke karamar hukumar Kiru domin magance matsalolin shaye-shaye da matasa ke yi a jihar kano.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci cibiyar domin ganin matsalolin da take fuskanta da kuma duba yadda za’a magance su.
Gwamnan yace gwamnatin sa zata Maida hankali wajen inganta rayuwar matasa domin su ne kashin bayan cigaban al’umma.
Yace shaye-shayen miyagun kwayoyi shi ke haddasa matsaloli na ta’addanci rashin tsaro da saura laifuffuka a cikin al’umma, a don haka yace zai inganta cibiyar ta hanyar samar da ababen more rayuwa da Kuma abincin da matasan dake gidan zasu rika ci.
Read Also:
Wannan ziyarana matsayin aikin Gwamnan na farko bayan rantsar da shi , yace gwamnati ta daukewa Iyayen da yaransu suke karɓar horo, tare da umartar Babbar Sakatariyar ta ma’aikatar mata da ta rubuto masa matsalolin da cibiyar take fuskanta domin magance wa nan da wata guda.
Da take nata jawabin Babbar Sakatariyar ma’aikatar mata ta jihar kano Dr. Sa’adatu Sa’idu Bala ta godewa sabon gwamnan saboda ziyarar da yakai cibiyar wanda tace hakan ya nuna yadda ya damu da halin da matasa ke ciki a jihar kano musamman batun kwacen waya da ake kashe mutane akai.
Babbar Sakatariyar ta bayyana cewa cibiyar tana taka rawa wajen gyara rayuwar matasa ta hanyar basu magani da koya musu sana’o’in dogaro da don inganta rayuwar su. Ta kuma ce cibiyar tana fuskantar matsaloli masu tarin yawa.
Tace ana gudanar da makarantar ne daga Naira 70 da ake biyawa yaran duk wata da kuma Naira dubu dari 5 da tsohuwar gwamnatin kano take ba su.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 8 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 49 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com