Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dokar bai wa ɗalibai bashin karatu ta ƙasa.
Mai magana da yawun Gwamnatin Tarayya, Dele Alake ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.
Read Also:
Sanarwar ta ce za a ajiye kuɗaɗen da za a rinƙa bayar da bashin ne a asusun Ma’aikatar Ilimi, kuma ɗaliban manyan makarantu ne kawai za su iya cin gajiyarsu.
Mako biyu da suka gabata ne ƙudirin, wanda shugaban Majalisar Wakilan Tarayya, Femi Gbajabiamila ya gabatar, ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dokokin Tarayya.
Dokar za ta bai wa ɗalibai ƴan asalin Najeriya damar karɓar bashi cikin sauƙi, wanda babu ruwa a tattare da shi daga Asusun Bayar da Bashin Karatu na Najeriya.
PRNigeria hausa I
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 2 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 43 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com