Home Labarai Gwamnatin jihar Kano ta gaggauta magance ayyukan daba a jihar – Majalisa

Gwamnatin jihar Kano ta gaggauta magance ayyukan daba a jihar – Majalisa

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi Kira ga Gwamnatin Jihar Kano data Umarci Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar da sauran hukumomin tsaro dasu Kai daukin gaggawa Unguwannin dake cikin Dala dake fuskantar matsalolin ‘Yan daba da masu kwace dake damun Yankin tsawon kwanaki.

Kiran ya biyo bayan kudurin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar Kuma wakilin Dala Hon Lawan Hussaini ya gabatar a zauren majalisar inda ya ce tsawon kwanaki batagari sun addabi Unguwannin na Dala da adakawa da kewaye da kwace da sare sare da tashin hankali kala kala a tsakar dare.

A cewar sa lamarin ya damu Al’ummar Yankin da tuni wasu sun fara kaura daga gidajensu saboda tsira da rayukansu kasancewar lamarin na janyo raunata mutane maza da mata..

Wakilin karamar Hukumar Rimin gado da Tofa Hon Muhammad Bello Butu-Butu da wakilin Ungoggo a majalisar Hon Aminu Saadu dana Dambatta da na Garko da Kuma na Takai cikin wadanda suka goyi bayan kudirin..

Shugaban Majalisar dokokin ta Kano Rt Hon Jibril Samaila Falgore ya bayyana amincewar Majalisar..

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp