Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da rushe dukkanin shugabannin hukumomi da ma’aikatu, cibiyoyi da kamfanoni mallakin gwamnatin tarayya, ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey a daren ranar Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ce, hakan yayi dai-dai da karfin ikon da kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa shugaban kasa don amfanin jama’a.
Read Also:
‘’Rushewar ba ta shafi kwamitoci da kuma Majalisun da aka jera a Jadawali na Uku, Sashi na 1, Sashi na 153 (i) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ba,’’ in ji sanarwar
Dangane da wannan an umarci shugabannin ma’aikatu, Hukumomi, Cibiyoyi, da Kamfanonin Gwamnatin tarayya da su mika ragamar wuraren da suke ga manyan Sakatarorin ma’aikatun domin su cigaba da kula da wuraren.
Ana kuma umurtar manyan sakatarorin su kai irin wadannan wasikun zuwa ga shugaban kasa ta karkashin ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Don haka, dukkan Ma’aikatu su tabbatar da bin wannan umarnin da zai fara aiki daga ranar Juma’a 16 ga watan Yuni, 2023.
An umurci manyan sakatarorin da su sanar da shugabannin hukumomin da abin ya shafa a karkashin kulawar ma’aikatu/Ofisoshinsu domin su bi umarnin cikin gaggawa.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 40 minutes 11 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 21 minutes 36 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com