Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya mayar da Barr Muhyi Magaji Rimin Gado kan kujerarsa ta shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar domin kammala wa’adin aikinsa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka aikowa Tambarin Hausa Mai dauke da da hannun Mai magana da yawun gwamnan Kano Dr. Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta ce gwamnan ya umarci Muhyi Magaji Rimin Gado da ya koma bakin aiki Nan take, a Wani mataki na yin biyayya ga umarnin kotu.
Idan dai za a iya tunawa gwamnatin baya karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta dakatar da Barr Muhyi kan wancen kujera sakamakon wasu zarge-zarge.
PRNigeria hausa












