Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin samar da kyakyawan wakilcin na ‘yan kasuwar jihar a majalisar zartarwa ta Kano.
Ta cikin wata sanarwar da mukaddashin mai magana da yawun gwamnan kano Hisham Habib ya aikowa PRNigeria, yace Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kasuwar Kano a gidan gwamnatin jihar.
Ya kuma ba su tabbacin kwamishinan kasuwanci da sauran mukamai da suka danganci yan kasuwa za su fito daga cikinsu don su sami wakilci a gwamnatinsa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa harkokin kasuwanci a jihar, ya kuma tabbatar wa ‘yan kasuwar kudirinsa na tallafa wa harkokin kasuwanci dai-dai da zamani.
Ya ce gwamnati za ta kuma rage cunkoso a birnin kano, ta hanyar bude sabbin wuraren kasuwanci, ya kuma bukaci matasan ‘yan kasuwa da su yi amfani da damar wajen bada hadin kai don cigaban jihar kano.
A jawabinsa Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam, ya jaddada kokarin gwamnati na ganin an dakile matsalar cin hanci da rashawa da jami’an hukumar kula da ababen hawa ta jihar da aka fi sani da KAROTA ke yi wadanda a zamanin gwamnatin da ta shude suka yi kaurin suna wajen karbar kudi a hannun yan kasuwar.
PRNigeria hausa












