Home Labarai Babu Amincewar Tinubu a karin albashin Shugaban kasa

Babu Amincewar Tinubu a karin albashin Shugaban kasa

Fadar shugaba kasa ta musanta Labarin karin kudin Albashin masu mukamun siyasa da Alkalai a Nijeriya.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar manema labarai da babban mai taimaka wa shugaba kasa Bola Tinubu a kan harkokin na musamman da yada labarai Dele Alake ya aikowa PRNigeria mai sauke da kwanan watan 22 ga watan Yunin, 2023.

Sanarwar tace Mun samu labarin da ke yawo cewa an yi ƙarin kashi 114 cikin 100 na albashin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, zaɓaɓɓun masu riƙe da muƙaman siyasa na tarayya da na jihohi da kuma jami’an shari’a.

Wannan labari ne mara tushe domin babu inda Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da batun ƙarin albashin, kuma babu inda aka gabatar da wannan ƙudiri a gabansa domin neman yardarsa.

Duk da cewa yana cikin kundin tsarin hukumar tattara kuɗin shiga da tsara kasafin kuɗi ta ƙasa RMAFC su ba da shawarar daidaita albashi da alawus ga masu rike da muƙaman siyasa da alƙalai, saidai hakan ba zai iya aiki ba har sai shugaban ƙasa ya yi duba tare da amincewa da shi.

Sannan kuma hukumar RMAFC, ta hannun Manajan Hulda da Jama’a, ta mayar da martani kan wannan labari na ƙarya da ake yaɗawa, ta kuma bayyana gaskiyar al’amarin.

Wannan labari mara tushe ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta da kuma wani ɓangare na kafafen yaɗa labarai, wanda hakan ya ƙara haifar da hatsarin da labaran karya ke haifarwa ga al’umma da kuma cigaban ƙasa baki ɗaya.

Ba shakka, an kirkiri wannan labarin karyar ne don mugun nufi ga sabuwar gwamnati, da nufin kawo tarnaƙi akan yunƙurin da ake yi na samar da gyara, da kuma kyakkyawar sheda da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da samu a tsakanin ƴan Najeriya a halin yanzu, sakamakon tafiyar da manufofinta cikin tsari mai inganci da zai samar da cigaba.

Ya kamata ‘yan jarida, kafofin yaɗa labarai, da jama’a duka su fahimci cewa duk labarin ayyukan gwamnati da batu akan manufofin ta da ba su fito a hukumance ba, labari ne mara tushe da yakamata a yi watsi da shi.

Ana kuma umartar ma’aikatan watsa labarai, a kowane lokaci, su dinga binciko tushen labaransu don tabbatar da sahihancin labaran da suke yaɗawa, wanda hakan shine alamar aikin jarida na ƙwarai.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp