Home Labarai Za mu sabunta ginin ganuwar Kano – Abba Gida-gida

Za mu sabunta ginin ganuwar Kano – Abba Gida-gida

Gwamnatin jihar Kano tace ta shirya tsaf domin gyara yin amfani da baguzen gine-ginen da aka rushe wajen sabunta ginin ganuwar Kano, a kokarin gwamnatin na maido da wuraren tarihi a jihar .

Wannan na kunshe ta cikin wata Sanarwar da Sakataren yada labaran gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa PRNigeria,  inda ya ce Abba Kabir Yusuf ya ce za a yi amfani da baraguzen wuraren da aka rushe wajen sake gina Badalar, kuma ana kira ga mutanen da ba su da alaka da inda aka rushe da su guji zuwa wurin domin yan sanda da jami’an hukumar Civil defense ba zasu saurarawa duk wanda aka kama ba.

“Mun zagaya birnin kano domin duba wuraren da aka ruguje, kuma mun yanke shawarar yin amfani da baraguzen wuraren da aka ruguje wajen gyara badalar birnin Kano domin adana tarihi, da kawata Kano da kuma mayar da wuraren wurin yawon bude idanu da dai sauransu”. Engr. Abba Kabir Yusuf yace.

“duk wanda ba ya cikin aikin rusau ya kamata ya nisanta kansa daga wurin, domin hukumomin tsaro ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace kan masu kutse da kuma wadanda suke sabawa ka’ida.” A cewar Abba Gida-gida

Gwamnan ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bin doka da oda tare da kai rahoto ga jami’an tsaro domin ci gaban zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp