Yunusa Yellow Ya Shaƙi Iskar Ƴanci

Matashin ɗan asalin jahar Kano mai suna Yunusa Yellow Kura, wanda ake tsare da shi tun a shekarar 2018 ya shaƙi iskar ƴanci bayan dogon lokacin da aka ɗauka ana shari’ar sa bisa zargin ɗauko wata budurwa mai suna Ese Oruru dake zaune a kudancin Nijeriya.
A baya dai an tsare Yunusa Yellow a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiyya a jahar Bayelsa kafin a dawo da shi jahar Kano.
An ruwaito cewa kakakin hukumar gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na jahar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya tabbatar da sakin Yunusa Ɗahiru Yellow, bisa kammala wa’adin da kotu ta yanke masa.
Tun da fari an zargi Yellow da auren Ese Oruru ba bisa ƙa’ida ba har aka tsare shi a jahar Bayelsa.
An gurfanar da Yunusa Yellow a gaban babbar kotun tarayya dake Yenagoa, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Jane Inyang, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 26 a gidan yari kan safarar budurwar.
Sai dai lauyoyin Yellow da suka haɗa da Abdul Mohammed SAN, Yusuf Ɗankofa, Huwaila Mohammed , Sunusi Musa da kuma Kayode Olaosebikan, sun ɗaukaka ƙara kan rashin amince wa da hukuncin.
Alƙalan Kotun ɗaukaka ƙarar ƙarƙashin jagorancin JS Iykegh , sun yi watsi da ɗaukaka ƙarar.
Sai dai sun bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa Yunusa Yellow na shekaru 26 ya saɓawa doka , inda alƙalan suka amince cewar Yunusa Yellow ya aikata laifin , sai dai sun rage shekarun zuwa shekaru 7.

Kuma a hukuncin da suka zartar sunce , zai fara ne daga ranar da aka tsare yellow, a shekarar 2018.

Yanzu haka dai Yello ya fita daga gidan yari, wanda tun abaya ake ta kiraye-kiraye ga shugabannin arewacin Nijeriya su shiga cikin maganar , sai ƙalilan daga cikin su ne suka taɓuƙa wani abu.
Yunusa Yellow , ya tsinci kansa ne cikin wannan hali sakamakon ƙaunar da matashiyar ke nuna wa Yellow, har ta baro garin su da kanta , kuma ta musulinta bisa amincewarta sannan suka yi aure.
Amma daga bisani lamarin ya sauya acan garin su inda suka ce wai safararra yayi zuwa Kano.
PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 7 hours 46 minutes 1 second,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 9 hours 27 minutes 26 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com