Kwararru masu binciken kwakwaf sun tabbatar da sahihancin faifen bidiyon da ke nuna tsohon gwamnan jihar Kano Dafta Abdullahi Umar Ganduje na cusa daloli a aljihunsa da aka ce cin hanci ne ya karba daga hannun wasu ‘yan kwangila.
Shugaban Hukumar Sauraren Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci ta Jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a wani taron yini guda kan yaki da cin hanci da rashawa a jihar.
Ta cikin jawabin nasa Muhyi ya ce, an tabbatar da sahihancin faya-fayan bidiyon.
Read Also:
Inda yace tun lokacin da aka saki hotunan bidiyon, jama’a ke ta kalubalantar hukumar da ta wanke gwamnan daga wannan zargi ko kuma akasin haka.
A shekarar 2017, Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta saki wasu hotunan bidiyon Ganduje na karbar kudadden da ake zargin cewa, na cin hanci ne, al’amarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen jihar.
Muhyi ya ce, tun a shekarar 2018 ne suka kaddamar da bincike kan lamarin, amma suka gaza zurfafa binciken Gandujen saboda a lokacin saboda rigar kariya da yake da ita a matsayinsa na gwamna.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 17 hours 1 minute 48 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 43 minutes 13 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com