Home Labarai Shuwagabannin Afirka ku mutunta Dimukradiyya – Tinubu

Shuwagabannin Afirka ku mutunta Dimukradiyya – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da doka-da-oda da kuma wanzuwar siyasa.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a taron tsakiyar shekara na gamayyar Kungiyoyin Haɗin Kan Afirka da na rassan ƙungiyoyin tattalin arzikin ƙasashen yankin Afirka da ke gudana a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.

Tinubu ya buƙaci mahukuntan ƙasashen na Afrika da su tabbatar sun mutunta batun sake sabunta mulkin dimokuraɗiyya.

Shugaban Najeriyar wanda kasance sabon shugaban kungiyar Ecowas, ya ce ya kamata a yi watsi da batun juyin mulki a faɗin nahiyar, musamman ma wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro da sauyin yanayi da kuma annobar korona.

Ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da kasancewar Yammacin Afrika sahun gaba wajen ɗaɓɓaka dimokuraɗiyya da kuma kyakkyawar shugabanci, ita ke gaba a yankin wajen amfani da hanyoyi da suka saɓa wa kundin tsarin mulki don sauya gwamnati.

Ya kuma yi gargaɗin cewa yawaitar kifar da gwamnatoci da ake samu a Afrika, na barazanar kawo rashin zaman lafiya da tsaro, da janyo talauci da ɗaiɗaita mutane wajen raba su da muhallansu.

”Tsakanin 2020 zuwa yanzu, Afrika ta fuskanci juyin mulki guda shiga da kuma guda uku wanda ba a samu nasara ba. Hakan na janyo tarnaki ga tsarin dimokuraɗiyyar mu a Afrika.

“Don haka, na ke kira ga ɗaukacin shugabannin Afrika da su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun mutunta ƴancin dimokuraɗiyya da kuma doka-da-oda don tabbatar da ɗorewar siyasa a nahiyar,” in ji Tinubu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp