Home Labarai Mun kama mayakan IPOB cikin wadanda muka tarwatsa – Sojojin Nijeriya

Mun kama mayakan IPOB cikin wadanda muka tarwatsa – Sojojin Nijeriya

Dakarun sojojin Nijeriya dake bibiyar mayakan da suka tserewa hari a Asaba, sun sami nasarar kame mayakan IPOB dauke da raunikan harbi a jikin su.

Wannan na zuwa ne bayan wani sumame da dakarun sojoji suka kai kan maboyar mayakan na IPOB a ranar asabar,

Ta cikin wata sanarwa da darakta yada labaran rundunar  Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya sake wallafawa a shafin hukumar na twitter, tace dakarun dake bin sahun mayakan na IPOB sun sake samun nasarar kwato makamai.

Idan za’a iya tunawa dakarun sojojin bataliya ta 63 karkashin shiyya ta 6 ta kai wani sumame a Safiya Asabar 22 ga watan Yulin 2023 a wani gungurmin DAJI dake Asaba.

Dakarun sun sami nasarar kama mutum daya dake dauke da rauni a jikin sa, gami da wasu mukamai, babu ran hawa Hudu, bindigu kirar  Double Barrel guns guda hudu, sai alburusan AK 47 guda biyar Magazines, da wasu Albusai na musamman guda 18 masu rai, sai wayoyin hannu guda shifa 6 da  Power bank guda 2, da kuma na’urar sadara kira  Boafeng Communication Radios guda shifa da waya kira Android, sai Computer kirar HP guda daya da tutocin kungiyar IPOB guda goma sha uku da dai sauran su.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp