Mahukunta na cigaba da jan hankulan Al’ummar Nijeriya kan cutar Anthrax

mai martaba Sarkin Suleja Muhammadu Auwal Ibrahim ya yi kira da hakiman masarautar da su kai rahoton rashin lafiyar dabbobi a yankunansu, tare da kauce wa cin naman da likitocin dabbobi ba su tantace lafiyarsa ba.

wannan na zuwa ne daidai lokacin da Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya NCDC ta ce har yanzu cutar Anthrax – da wasu dabbobin ƙasar ke fama da ita – ba ta yaɗu zuwa ga bil-adama ba.

Shugaban hukumar, Dakta Nasir Ahmed yayin da yake ganawa da gidan Talabishin na kasar NTA ne ya bayyana cewa hukumar na ci gaba da lura tare da sanya idanu, musamman a garin Suleja inda cutar ta fara ɓulla a ƙasar.

Gwamnatin ƙasar ƙarƙashin ma’aikatar lafiyar ƙasar na ƙarfafa gangamin wayar da kai kan alamomin cutar da yadda za a kauce wa ɗaukar ta, musamman a masarautar Suleja da ke jihar Naija.

Tuni dai gwamnatin ƙasar ta bayyana sayen alluran riga-kafin cutar domin yi wa dabbobi a garin Suleja, inda cutar ta fara ɓulla.

Dabbobi na gida da na daji na kamuwa da cutar ne idan suka shaƙe ta daga ƙasa wadda ke ƙunshe da ƙwayoyin cutar ko kuma suka ci ciyawa ko shan ruwan da ke ɗauke da ita.

Dabbobin da suka fi kamuwa da cutar sun haɗa da shanu da tumaki da awaki da kuma barewa.

Haka kuma likitoci sun ce mutane na kamuwa da cutar a lokacin da suka yi cuɗanya da dabbobin da ke ɗauke da cutar ko kuma suka taɓa wani abu da ya fito daga jikin dabbobin.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 11 hours 37 minutes 20 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 13 hours 18 minutes 45 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com