Home Labarai ‘Yan bindiga sun hallaka mutum daya a jihar Katsina

‘Yan bindiga sun hallaka mutum daya a jihar Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar katsina dake arewa maso yammacin Nijeiya ta tabbatar ta mutuwar mutum daya sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai karamar hukumar Kankia ta jihar.

kakakin hukmar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni ƴan sanda suka fara bincike kan lamarin domin kamo waɗanda ke da hannu a kai harin.

‘yan bindigan sun harbi mutumin ne lokacin da suka kai hari wani rukunin gidaje da ke unguwar low-cost kusa da babban asibitin karamar hukumar a daren Asabar.

Wani ganau ya bayyana cewa ƴan bindigar sun zo ne a kan babura, inda suka yi wa rukunin gidajen dirar miƙiya tare da harbi kan mai uwa da wabi, abin da kuma ya janyo mutuwar mutumin mai suna Alhaji Ibrahim Baraya Solo.

Bayan kashe mutumin ne, sai maharan suka tsere tare da barinsa cikin jini.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp