Shalkwatar tsaron kasa ta yi watsi da masu kira kan sojojinta da su yi katsalandan a tsarin dimokradiyyar kasar nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Asabar, in da tace sojojin kasar sun nuna rashin jin dadinsu kan wani labari da ake yadawa a yanar gizo kan cewa akwai wasu matsaloli game da batun jin dadi da walwalwa na sojojin kasar.
Sanarwar ta ce shugaban sojin kasar Janar CG Musa ya kara jaddada biyayyarsa ga Shugaba Tinubu inda ya ce ba zai kauce wa aikinsa da kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tsara ba.
“Kiraye-kirayen da ake yi kan sojoji da su yi katsalandan a dimokradiyya rashin kishin kasa ne, da mugunta da kuma yunkurin kawar da hankalin sojojin Nijeriya daga gudanar da ayyukansu da kundin tsarin mulki ya tsara,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Read Also:
“Ganin cewa rundunar sojin Nijeriya tana mayar da hankali wurin kyautata wa dakarunta, ba ma son duk wani yunkuri na wani ko wata kungiya da za ta harzuka Sojojin Nijeriya masu bin doka domin su tunkari sauyin gwamnati wanda kundin tsarin mulkin kasar bai amince da shi ba.
“Muna so mu bayyana cewa ba shakka sojoji suna farin ciki kuma sun fi dacewa a karkashin mulkin dimokradiyya kuma ba za su shiga duk wani aiki na zagon kasa ga dimokradiyyar da aka samu a kasarmu ba,” in ji sanarwar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen dake Nahiyar Afirka ke fuskantar katsalandan da sojojin ke yi a harkokin Damukradiyya abin da wasu ke kallon shine Mafita ga nahiyar, in da nasan harkokin yau da kullum da cigaban Al’umma ke Allawadai da katsalandan din kasancewar shike sake mayar da nahiyar ta Afrika baya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 2 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 43 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com