Home Labarai Dakarun sojoji sun jikkata sananne dan ta’addan Dogo Gide

Dakarun sojoji sun jikkata sananne dan ta’addan Dogo Gide

Wani rahoton binciken jaridar PRNigeria ya tabbatar mata da cewa dakarun soojin Nijeriya sun sami nasarar raunata Dogo gide, dan ta’addan da ake nema ruwa a Jallo a jihar Zamfara.
Dogo gide ya tsallake rijiya da baya, da raunikan harbin bindiga a jikin sa, bayan wani hari da dakarun soji suka kai a wani bangare na kakkabe maboyar ‘yan ta’addan dake jihar Zamfara.
Wata majiya daga rundunar ta tabbatarwa da PRNigeria cewa sojojin sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan dake na jihar dake kauyukan Dansadau, Mai Tukunya da Babban Doka.
“Yayin gudanar da atisayen dakarun sun mamaye yankin Ya’u Sarkin Pawa gida Dogo Gode, inda suka bincika gidan suka kuma tarwatsa shi.
“An sami kayayyaki a gidan Dogo Gide, da suka hadar da kayan dinka kayayyakin sawa na sojoji da sauran jami’an tsaro, kayan fashewa na (IEDs); wani karamin wurin shan magani domin bayar da taimakon gaggawa ga ‘yan bindiga, baburan hawa guda 5 da kekunan dinky, wanda duk dakarun suka bankawa wuta.
“Dakarun karkashin OPHD sun kuma sami nasarar tarwatsa ‘yan ta’addan dake kauyukan Malele, Mutunji, Kwana, Kamatso, Kememe, Kango wanda ke matsayin maboya ga ‘yan ta’addan.
“haka kuma sojojin sun bankado gami da tarwatsa maboyar ‘yan bindigar a kauyukan Koli, Bakin Dutse da Farin Ruwa inda suka sami nasarar kwato Baburan hawa da wayoyin hannun guda 4” kamar yadda majiyar ta tabbatar.
PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp