Shugaban ƙasar Nigeria Bola Tinubu ya amince da nadin Muhammad Abba Isa a matsayin babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin masu bukata ta musamman.
A cewar wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis, yace nadin na cikin kudirin Tinubu na tabbatar da cewa kowane bangare na al’umma ya samu isasshiyar dama a gwamnatin sa.
Read Also:
“Muhammad Abba Isa fitacce ne wanda ya kwashe sama da shekaru 10 yana bada shawarwarin yadda za’a inganta rayuwar Masu bukaci ta musamman a gida Nigeria da kasashen waje,” in ji sanarwar.
“Sabon mai taimaka wa shugaban kasa ya kammala karatunsa kan harkokin mulki a jami’ar Maiduguri, inda kuma yayi Digirin na biyu a wannan fannin a dai jami’ar ta Maiduguri a shekarar 2017.
Shugaban ya bukaci sabon mai bashi shawara da ya samar da hanyoyin da za a bi don shigar da masu bukata ta musamman cikin manufofi da shirye-shiryen dukkan ma’aikatu, sassan da hukumomin gwamnatin tarayya tare da yin aiki kafada da kafada da kananan hukumomi don aiwatar da shirin, don inganta rayuwar su.
PRNigeria Hausa