Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya koma gida bayan ya cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi.
Mai magana da yawun Gidan Yari na Kuje da ke Abuja, inda aka tsare Mista Emefiele, ya tabbatar da cewa an saki tsohon gwamnan a yammacin Juma’a.
Tun a ranar 22 ga watan Nuwamba ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da belinsa kan naira miliyan 300 tare da gabatar da mutum biyu da ke da kadarori a unguwar Maitama da ke birnin na Abuja. Haka nan, kotun ta umarce shi da miƙa mata dukkan takardunsa na tafiye-tafiye.
Read Also:
Lamarin na zuwa ne bayan wani rahoto da mai bincke na musamman, Jim Obazee, ya zarge shi da karya dokar kwangila da sayen kayayyakin gwamnati.
Rahoton Obazee, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa a watan Yuli don ya binciki CBN a ƙarƙashin mulkin Emefiele, ya zarge shi da amfani da wakilansa wajen sayen Bankin Union, da kuma yin amfani da ƙarfin ikonsa a cinikin bankunan Polaris da Keystone.
Gwamnatin Tinubu na zargin tsohon gwamnan wanda ta dakatar a watan Yuni da aikata almundahanar kuɗi naira biliyan 1.2, zargin da ya musanta.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 1 minute 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 43 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com