Wasu hare-haren ‘yan bindiga kan kauyuka sun yi sanadiyya mutuwar a kalla mutane 160 a tsakiyar Nijeriya a cewar mahukunta ranar litinin.
Adadin ya karu kan rahoton da rundunar sojin kasar ta fitar na cewa mutane 16 ne suka mutu a bias wani rikicin kabilanci da aka kwashe shekaru ana gudanarwa.
A yayin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na AFP shugaban karamar hukumar Bokkos, a jihar Filato, Monday Kassah ya ce an tabbatar da mutuwar mutane 113 a daren litinin.
Read Also:
Yace yan bindigar sun kai hari a kalla garuruwa 20 ma bambanta, inda suka taba gidajen al’ummar dake rayuwa a garuruwan a cewar, Kassah.
“Mun samu mutane sama da 300 da suka jikka” wadanda yanzu haka an kaisu asibitocin Bokkos, Jos da barkin ladi.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta red cross ta ce mutane 104 ne suka mutu a kauyuka 18 na Bokkos.
Haka kuma an ruwato cewa mutane 50 ne suka mutu a kauyu mabambanta dake karamar hukumar barkin ladi, kamar yadda Dickson Chollom, guda cikin ‘yan majalisar jihar.
Dickson yayi Allah wadai da harin, inda ya bukaci jami’an tsaro su dauki matakin gaggawa kan lamarin.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 16 hours 41 minutes 38 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 23 minutes 3 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com