Home Labarai Tinubu ya maye gurbin TSA da CRF

Tinubu ya maye gurbin TSA da CRF

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta rufe asusun ajiyar kudi na kasa wato (TSA) da gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da shi wajen tara kudaden shiga.

Sai dai gwamnatin tarayya ta umurci dukkan ma’aikatu, da hukumomi da su tura kashi 100 na kudaden shiga zuwa asusun ajiyar kudaden shiga na yau da kullun, wani bangare na asusun tattara kudaden shiga (CRF).

CRF shine sabon asusu inda a yanzu gwamnatin Tinubu za ta karba tare da hada kudaden shigarta a cikin sa.

Hakan ya zo ne bisa wata takardar mai kwanan watan 28 ga Disamba, 2023, wadda ma’aikatar kudi ta fitar a ranar Talata, 2 ga Janairu, 2024.

Wannan umarni dai ya rufe asusun baitul mali na bai daya da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da shi.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp