Home Labarai Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce ta Karfi Kaddara

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta ce ta Karfi Kaddara

Jam’iyyar APC a Kano sun tace sun rungumi ƙaddara game da hukuncin kotun kolin Najeriya da ta tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.

Sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Zakari Sarina, ne ya bayyana haka ta cikin wata hira da gudanar da kafar yada labarai ta BBC, in da ya ce sun karɓi ƙaddara, suna kuma fatan hakan ya zame musu alkairi.

”Allah ya sa hakan ne ya fi alkari, kuma muna bai wa ‘yan jam’iyar mu na APC da sauran al’ummar jihar kano hakuri, tare da kiran a zauna lafiya”, in ji shi.

Ya ce kuma suna kyautata wa Allah zato cewa tabbas hakan zai zama alkairi a gare su.

”A yanzu muna cikin alhini, kuma bai kamata mu ɗauki mataki a lokacin alhini ba, amma idan ƙura ta lafa, za mu zo mu zauna, mu shirya domin tunkarar zaɓen 2027”.

Tun da farko dai jam’iyyar ce ta yi nasara a kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara, kafin yau kotun ƙoli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan farkon.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp